Shafar fuska bayan addu’a

Egypt's Dar Al-Ifta

Shafar fuska bayan addu’a

Tambaya

Mene ne hukuncin shafa fuska da hannunwa biyu bayan addu’a, ganin cewa akwai wadanda suke cewa hakan bidi’a ne mai muni?

Amsa

Daga hannu a lokacin da ake yin addu’a, da shafa fuska da su bayan kamala addu’a a cikin sallah, ko ba a cikin sallah ba sunna ne, wannan shi ne ra’ayin jamhur din malamai.

Allah Madaukakin Sarki ya umurce mu da yin addu’a, ya kuma yi mana alkawarin zai amsa; mai girma da daukaka ya ce: (Ubangijinku ya ce: ku roke ni, zan amsa maku..) [Gafir: 60], a cikin sunnonin da aka so a yi su a lokacin da ake addu’a akwai daga hannuwa, da shafar fuska da su idan a n gama addu’ar, sawa’un a cikin sallah ne, ko a wajenta, wannan abu ne da mazhabobin Hanafiyya da Shafi’iyya, da Hanbaliyya suka hadu akan halaccinsa; saboda Hadisin Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) da yake cewa: (Idan za ku roki Allah, ku roke shi da tafukan hannayenku, kada ku roke shi da bayansu, sannan ku shafa fuskokinku) [al- Hakim].

Share this:

Related Fatwas