Tasirin da yada jita- jita yake yi ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Tasirin da yada jita- jita yake yi a rayuwar al’umma

Tambaya

Mene ne abin da ya wajaba Musulmi ya aikata game da jita- jitar da ake yadawa a cikin al’umma?

Amsa

Addinin Musulunci ya rufe kofa da mabubbugar jita- jita, tun da ya wajabta wa Musulmai yin bincike da tabbatar da labarai kafin a dora hukunci akansa, ya bayar da umurni a mayar da al’amurra zuwa ga masu ita masu ilimi tun kafin ya yada, ko ya yi magana akai, Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Ya ku wadanda kuka yi imani, idan har wani fasiki ya zo maku da wani labari, to ku bincika, gudun kada ku auka wa wasu mutane cikin rashin sani, ku dawo kuna nadama akan abin da kuka aikata) [al- Hujrat: 6].

Haka ma Musulunci ya hana ji da yada jita- jita, Allah mai girma da daukaka ya kuma zargi masu gulma da masu yama- didi da yada jita- jita da fitina; Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Idan ma da sun fita jahadin tare da ku, da fitar tasu ba za ta kara maku karfi ba, hasali ma za su kawo rudani ne a cikinku, ko su yi gaggawar kirkirar fitina, su kuma yada ta a tsakaninku, kuma a cikinku akwai wadanda suka jahilci mummunar niyyarsu, ta yiwu su yaudare su da maganganunsu, ko su saurari kiran da suke yi na fitina saboda raunin da suke da shi, lallai Allah yana da cikakkiyar masaniya da wadannan munafukan da suke cutar da kawunansu, da barnar da suka kulle a cikin zukatansu) [at- Tauba: 47].

Share this:

Related Fatwas