Katange kayan masarufi ko wani abu ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Katange kayan masarufi ko wani abu makamancin haka

Tambaya

Mene ne sakamakon mai yin babakere a kan kayan masarufin da ake sanyawa tallafi tare da katange kayan domin sayarwa a kasuwar bayan fage.

Amsa

Samarwa kai ko rabauta da kayan masarufin da aka sanyawa tallafi ga wanda bai cancanta ba, ko mamaye kayan ta hanyar da bai dace ba, ko sayar da kayan a kasuwar bayan fage, ko kuma killace kayan to haramun ne a shari’ance, hakan na daga cikin manyan laifuffuka, saboda hakan  cutarwa ne kuma yiwa hakkokin mutane ta’addanci ne, haka nan yiwa dukiyar jama’a illa ne, kuma cin dukiyar mutane ne ba tare da hakki ba, kuma hakan ya sabawa umurnin shugaba, wanda Allah Ta’ala ya wajabta da a yi masa biyayya in dai ba wurin sabo bane, idan akayi la’akari da yiwa Allah Ta’ala da Manzonsa S.A.W. biyayya,  to Allah Ta’ala ya ce: (Ya ku wadanda ku ka yi Imani ku yiwa Allah biyayya ku yiwa Manzonsa biyayya sannan ku bi majibinta al’amuranku) {An’nisa:59}

To duk wadanda suke aikata wannan danyen aikin na yin babakere kan kayan masarufin da aka sanyawa tallafi ciki tare da sayar da kayan, to shari’a tayi musu tanajin narko mai zafi domin su wa’azantu, domin su koma kan shiriyansu ta hanyar dena aikata wannan barnar.

 An karbo daga Jabeer bin Abdallah Allah ya kara mu su yarda cewa Manzon Allah S.A.W. ya ce: (Ya Ka’abu bin Ujrata, ka sani cewa duk wanda naman jikinsa ya tofu daga haram ba zai shiga Aljanna ba, wuta ce ta dace da shi, Ya kai Ka’abu bin Ujrata, mutane kashi biyu ne wurin karshen makoma, akwai wanda ke sayan kansa domin ya ‘yanta ta, da kuma mai sayan kansa domin ya tozartar da ita) {Imam Ahmad ne ya ruwaito wannan Hadisin}.

Duk mai aikata irin wannan mummunan aikin ya cancanci ukuba karkashin dokan da aka sanya, tare da kuma hukuncin da Allah ya yiwa mai aikata irin hakan a ranar lahira.

Share this:

Related Fatwas