Ma’anar Jahiliyya

Egypt's Dar Al-Ifta

Ma’anar Jahiliyya

Tambaya

Mene ne ma’anar da Alkur’ani da Hadisai suke bai wa kalmar Jahiliyya? Kuma ta yaya kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi suka yi mummunar amfani da wannan kalma wajen kafirta al’umma?

Amsa

Kalmar jahiliyya a cikin Alkur’ani da Hadisai tana nuni ne zuwa ga lokacin da ya gabaci aiko Annabin shiriya, shugabanmu Annabi Muhammadu (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), zamanin da al’adun shirka da bautar gumaka, da halatta abubuwa marasa kyau, wannan kuma ba abu ne da ya kebanci Larabawa kawai ba, hasali ma ya game dukan al’ummomi kafin aiko Annabi Muhammadu (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), Allah Madaukakin Sarki yana cewa: (Ku zauna a gidajenmu, kada ku bayyana tsaraicinku, bayyanawa irin yanda mutanen zamanin jahiliyyar mutanen farko suke yi) [al- Ahzab: 33], ma’ana, kada ku aikata irin yanda matan zamanin jahiliyyar farko suke yi, wato zamanin da ya gabaci zuwa addinin Musulunci, kuma kowa ya san cewa wannan zamanin ya tuke da zuwan Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) da aiko shi da sako da Allah ya yi, kuma ba a fita daga Musulunci sakamakon aikata manyan zunubai da laifuffuka, sai dai duk da haka kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi sun dauki wannan kalma a wannan zamani a matsayin kofar da suke bi su kafirta Musulmai ba bisa kan ka’ida ba, suna riya cewa wai al’umma suna rayuwa ne a zamanin jahiliyya, koda kuwa suna yawan maimaita kalmar “La’ilaha illalLahu, Muhammadur RasulilLahi”, suna kuma tsayar da sallah, gaskiyar al’amari ita ce: wadannan kungiyoyi sun yi amfani da wannan kalma ce wajen biya wa kawunansu bukatu na kafirta al’umma, inda suke yunkurin lullube aikinsu da mayafi na shari’a, abin da zai sanya a zaci cewa su kadai ne suke da gaskiya, kuma su ne kawai Musulmai, lallai da haka suna bata surar Musulunci da Musulmai ne.

Share this:

Related Fatwas