Ma’anar bidi’a ta bata

Egypt's Dar Al-Ifta

Ma’anar bidi’a ta bata

Tambaya

Mene ne inganntaccen ma’anar bidi’a ta shari’a? shin ko duk abin da Annabi SallaLahu AlaiHi wa sallam bai aikata ba ya kasance bata? 

Amsa

Ana danganta kalmar “Bidi’a” ne akan duk wani abu da ke zama sabo ne kuma kirkirarre a cikin addini bayan ya cika, amma a cikin shari’a malamai sun bayyana ma’anar bidi’a ta hanyoyi guda biyu.

Na farko: Shi ne maganar Ezz bin Abdul Salam, in da ya lura da cewa lallai duk abinda Annabi SallaLahu AlaiHi wa sallam bai aikata ba bidi’a ne, sannan ita bidi’ar ta kasu zuwa: bidi’a wajiba, bidi’a haramtacciya, bidi’a manduba, da kuma bidi’a makaruha, sai bidi’a mubaha, hanyar sanin wadannan kashe- kashen shi ne a sanya su a ma’aunin shari’a, idan suka shiga cikin layin kyawawan abubuwa to sun zama wajibi, idan kuma suka shiga layin haramci to sun kasance ababen haramtawa, to haka dai lamuran suke.

Na biyu: Shi ne takaita bidi’a a matsayin abun zargi ne kawai, kuma haramtacciya ce, kuma akan haka jamhorin malaman fikihu suka tsaya a kai, abin da ke da muhimmanci garemu anan shi ne, yin ittafaki akan bidi’a wacce take abar zargi ce, wanda duk mai aikatawa to ya aikata sabo a shari’ance. Amma anan shin duk abin da Annabi SallaLahu AlaiHi wa sallam bai aikata ba yana daga cikin bidi’ar da ake kin ta ko zargin mai aikatawa? A zahirin gaskiya ba haka bane, hakika al’umma ta kirkiri kyawawan ayyukan na alheri ma su yawa bayan Annabi SallaLahu AlaiHi wa sallam, don haka ne ma Imam Ghazali yake cewa: (Ba duk abinda aka kirkira ne ke zama abin hanawa ba, kai wani abin ma da aka hana kan kalubalanci abinda yake tabbatace a sunna, wanda kuma hakan ke dauke hukuncin wani lamari na shari’a). To a bisa haka ne ake iya fahimtar bidi’a bisa ingantaccen hanya.

Share this:

Related Fatwas