Hadisi Da’ifi da Maudu’i

Egypt's Dar Al-Ifta

Hadisi Da’ifi da Maudu’i

Tambaya

Wani Hadisi ne ale kira da Da’ifi, kuma menene banbancinsa da Maudu’I, shin ya halasta ayi aiki da hadisai da’ifai “masu rauni” kuma a wani bangare ya kamata?

Amsa

Shi hadisi “Da’ifi” wato mai rauni shi ne hadisin da ya rasa wani sharadi guda daya ko fiye da haka daga cikin sharudan hadisi sahihi ko hasani, mai rauni kuwa wato (Da’ifi) shi ne wanda ya samu rauninsa sakamakon rauni na illa a wurin abinda mai ruwayansa ya tabbatar, amma ba tare da anyi suka ga adalcin shi mai ruwayar ba, amma wanda ake zargi da rashin adalci a akaran kansa, to ba a la’akari da shi bare har a amshi abinda ya ruwaito, kamar ace ana zarginsa da cewa shi  makaryaci ne, ko mai kirkiran zance, wato dai mai yin karya da gangan ga Manzon Allah SallaLahu AlaiHi wa sallam, a kan sa ne Annabi SallaLahu AlaiHi wa sallam yake cewa: (Duk wanda ya kirkiri karya ya jingina zuwa gareni da gangan, to ya yiwa kansa mazauni a cikin wuta), Anyi ittifaki a kansa, Malamai sun bayyana cewa karancin kiyayewan mai ruwaya ka iya kaiwa ga kasancewar hadisin da ya ruwaito mai kyau bisa la’akari da wasu hanyoyin ruwayan hadisin na daban, don haka sai a dauka ayi amfani da shi a hukunce hukuncen shari’a a duk lokacin da aka bukace shi, don haka ana amfani da hadisi da’ifi ta ko’ina a sashen mafificin ayyuka, kamar tsoratarwa da kwadaitarwa wurin ambaton lada ko zunubin abin da ke  da asali tabbatacce kamar dai yiwa iyaye biyayya, da yin tasbihi, da yin azkaru, da wasu ayyukan kyawawa.

Amma shi hadisi maudu’i shi ne wanda aka kirkiri karya aka jinginawa Manzon Allah SallaLahu AlaiHi wa sallam, to irin wannan ba a la’akari da shi ta dukkan fuskoki ko hanyoyi, kuma bai samun dagomashi na karfi daga waninsa, ba kuma a yin ruwayarsa sai dai a bayyana cewa kirkirarre ne, ba kuma a aiki da shi a wuraren mafifitan ayyukan ko a hukunce hukunce na shari’a.

Share this:

Related Fatwas