Zikiri da adadi

Egypt's Dar Al-Ifta

Zikiri da adadi

Tambaya

Mene ne hukuncin yin zikiri da wani adadi?

Amsa

Allah mai girma da daukaka ya umurce mu da yawaita ambatonsa, Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Ya ku wadanda kuka yi imani ku ambaci Allah da yawa) [al- Ahzabi: 41], shi Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) wahayi kawai ake yi masa; alal misali, a lokacin da ya karantar da mu yanda za mu yi tasbihi a karshen kowace sallah, ya karantar da mu cewa mu yi tasbihi sau talatin da uku, mu kuma yi tahmidi sau talatin da uku, mu kuma yi kabbara sau talatin da uku, wannan adadin yana da sirri a cikin halitta, idan bawa ya yi wannan adadi zai isa zuwa ga biyan bukata, koda babu komai sai yi wa Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam)  biyayya a abin da hankali ba zai iya hararo ma’anarsa ba ya isa, idan Allah ya yi masa fatahi, alhamdu lilLahi, idan ma ba a yi masa fatahi ba, ya isa a ce ya yi koyi da zababben Annabi Muhammadu (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), shi zikiri a kowane yanayi abu ne mai kyau, ana kuma son a takaita da adadinin da Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya bayyana a wasu wurare, yin haka sunna ne, yana kuma kai wa zuwa ga bude wasu sirrorin halittu da ba a sani sai da haka.

Share this:

Related Fatwas