Aikin malamai

Egypt's Dar Al-Ifta

Aikin malamai

Tambaya

Shin wajibi ne a kowane lokaci a koma zuwa ga malamai, ko kuwa abu ne mai yiwuwa mutum ya tambayi kansa ya bi abn da ya karanta kawai?

Amsa

Malamai su ne Allah Madaukakin Sarki ya ajiye su domin su zama masu bayar da kariya ga hukunce- hukuncen addininsa, saboda haka dole ne su bayyana wa mutane sharrin duk wani mai sharri; saboda su yi masu gargadi, musamman idan sun kasance cikin masu kira zuwa ga kafirci da batar da suke a kai, dalilai masu yawa sun zo akan haka, a cikinsu akwai inda Allah Madaukakin Sarki yake cewa: (Ka fada masu lokacin da Allah ya yi alkawari da wadanda aka ba su littafi kan cewa lallai ne ku bayyana shi ga mutane, kada ku kuskura ku boye, sai suka yi watsi da shi a bayansu, suka sayar da shi da kudi kadan, ai kuwa tir da wannan sayarwa da suka yi) [Ali Imran: 187].

Imam al- Kurdabiy ya bayyana cewa wannan ayar ta game duk wani wanda aka bas hi ilimi wani abu na Alkur’ani, duk wanda ya san wani abu, to dole ne ya sanar da shi ga wasu, ahir dinku da boye ilimi, domin yin haka halaka ne. Muhammad Bn Ka’ab ya ce: Sam bai halatta malami ya yi shiru akan abin da ya sani ba, haka ma bai halatta jahili ya yi shiru yak i tambaya akan abin da ya jahilta ba, Abuhuraira ya ce: ba domin alkawarin da Allah ya dauka da masu ilimi ba da ban bayyana maku komai ba, sannan ya karanta ayar: (Ka fada masu lokacin da Allah ya yi alkawari da wadanda aka ba su littafi..)

Saboda haka, dole ne a koma zuwa ga malamai cikin duk wata mas’ala da ba a gane ba, a asali su ne masu ruwa da tsaki, kuma su ne “Ahlaz zikri” Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Ku tambayi masana idan har dai ku ba ku sani ba) [an- Nahli: 43], malami kuma shi ne wanda ya cika kamalar fahimtar shari’a, da kamalar fahimtar yanayin da mutane suke ciki, da halayensu da al’adunsu.

Share this:

Related Fatwas