Tambayar malamai

Egypt's Dar Al-Ifta

Tambayar malamai

Tambaya

Wane irin kallo masu tsattsauran ra’ayi suke yi wa ilimi da malamai?

Amsa

Lallai manhajin da Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya assasa, ya kuma ginu a zukatan mabiyansa shi ne rashin gabatar da mummunar fahimta akan aiki da addini da aiki da addini, hasali ma ya hana yi wa gaskiya giman kai, da ganin cewa fahimtar ka ce kawai fahimta; a duk sanda aka gabatar wa sahabban Annabi (Allah ya kara yarda da su) da wata mas’ala, sai su rika kakkaucewa gudun kada su yi magana akan addini ba tare da ilimi ba.

Amma duk da haka za ka samu a duk sanda aka bijiro wa masu tsattsauran ra’ayi da wata ma’ana, ko wani aiki, za ka samu sun kulle cewa fahimtarsu ita ce gaskiyar da babu wata sai ita, saboda haka suke nuna ta’assubanci mai tsanani akanta, sama da ta’assubanci da wasu mabiya mazhabobi suke yi, daga nan kuma sai al’amarin ya sauya ya zama rikici, da fada da jubar da jini da barna a bayan kasa.

Babu shakka maganin haka shi ne komawa zuwa ga malamai masana ilimi da Allah ya azurta su da fahimtar addinin Allah Madaukakin Sarki, wadanda suke da manhaji, har abin ya zama masu jiki, inda haka zai ba su daman cancanta na su yi duba a cikin nassoshin shari’a, Allah mai girma da daukaka ya ce: (Da a ce za su mayar da shi zuwa ga manzon Allah da majibinta al’amarin cikinsu, da malamai masu istimbadi sun san shi) [an- Nisa’i: 83].

Share this:

Related Fatwas