Waliyi da walicci

Egypt's Dar Al-Ifta

Waliyi da walicci

Tambaya

Wane ne waliyi? Ta yaya Musulmai suka yi mu’amala da mas’alar walicci da mai da’awar walicci?

Amsa

Lallai shi waliyi bawa ne nagartacce da yake jibintar Allah wurin ibada da kuma kusantarsa, sai Allah ya jibinci lamarinsa da rahamarsa da ludufinsa da kiyayewansa, matsayin waliyai dai tabbatacce ne a Kitab wal Sunnah, Allah Ta’ala yana cewa: (Lallai su waliyan Allah babu tsoro a tare da su kuma ba sa yin bakin ciki[Yunus:62] Manzon Allah SallallaHu AlaiHi Wasallam ya ce: (Lallai daga cikin bayin Allah akwai wadansu mutane da su ba Annabawa bane, kuma ba shahidai bane amma Annabawa da shahidai suna burin inama su ne a matsayinsu ranar Alkiyama, saboda matsayin da Allah ya ba su) sai suka ce: Ya Manzon Allah: ko za ka bamu labari akansu? Sai ya ce: (Wadansu mutane ne da suka so juna saboda Allah ba tare da sun hada dangantaka ba a tsakaninsu, ko kuma wata dukiya da take gudana a tsakaninsu, Na rantse da Allah lallai a fusakunsu akwai wani irin haske, kuma suna kan wani haske ne, ba sa jin tsoro a lokacin da mutane suka tsorata, kuma ba sa yin bakin ciki a lokacin da mutane suka yi bakin ciki), sai ya karanta ayar: (Lallai su waliyan Allah babu tsoro a tare da su kuma ba sa yin bakin ciki) [Dawud].

Hakika an tambayi Manzon Allah SallallaHu AlaiHi Wasallam: Su waye waliyan Allah? Sai ya ce: (Su ne wadanda idan aka gansu ake tuna Allah) [Nisa’i] hakika Musulmai sun yi ta’amuli tare da mas’alar wilaya da gasgatawa da tabbatarwa da kuma girmama su waliyan saboda kusancinsu ga Allah, sannan kuna sun kalubalanci mai ikirarin waliyantaka da bijirewa da toshe haskensu da gurabunsu bisa karyarsu.

Share this:

Related Fatwas