Hakikanin ma’anar jihadi a musulunci
Tambaya
Shin an jingine ko hana yin jihadi a wannan zamanin,sannan kuma shin ya wajaba a dawo da raya yin jihadin ko aiwatarwa a yanzu? Kuma alhakin hakan ya rataya a wuyan waye?
Amsa
Shi jihadi farilla ne da aka hukunta da babu hanyar jinginewa - ballantana kuma sokewa - wannan wajibcin yana da dokoki da tabaibayoyi wanda majibinta al’amura suka sanya kuma suka iyakance, daga cikin al’ummar musulmai, ba wani al’amari ne da aka barshi a asake haka kawai ba, wadancan takunkumomin sune malaman shari’a suka ambata a littafai da daman gaske, idan har ba a kula da wadancan ka’idojin na jihadi da manufofinsa na shari’a ba, to ba a kiransa da sunan jihadi, domin kuwa hakan sunansa barna, ko zalunci da ha’inci, ba duk yaki ne ke kasancewa jihadi ba.
Don haka abinda kungiyoyi na ‘yan ta’adda a kasashen musulmai suke yi na kisa, ko a kasashen da ba na musulmai na yin kunan bakin wake, ko wani aiki daga cikin ayyukan rushe kasa sakamakon bin manhajin hada fada da bata to haramun ne a shari’ance, kuma laifi ne a mutumtuka da kuma doka, duka wannan wani sashe ne na barna wanda ake mayarwa mai aikata hakan da martani mai karfi, hakika nassosin shari’a masu girma sun zo da al’amari na kangewa, kuma ya wajaba a yaki masu zalunci idan har basu tuba daga aikata munanan ayyuakansu ba, wadanda suka shafi musulmai da wadanda ba musulmai ba.
Amma tsinkaya lafazin jihadi akan abin da suke aikatawa ba wani abu bane face nau’i ne na badda kama da wala-wala don da hakan ne suke rudan masu karancin tunani domin gamsar da su da wadannan hanyoyin na barna da kuma yin barna, ana kallon irin wadannan mutanen a matsayin mabarnata da za a yakesu idan har suna da mummunar manufa har sai idan sun dawo kan shiriyansu.