Dimaucewar kungiyoyin ‘yan ta’adda

Egypt's Dar Al-Ifta

Dimaucewar kungiyoyin ‘yan ta’adda

Tambaya

Wani abu ne yafi bayyana   dimaucewar ‘yan ta’adda wurin fahimtar  jihadi?

Amsa

Dukkan wadannan kungiyoyin na ‘yan ta’adda wurin fitar da zantuttukan na addini to muryarsu da ya ce duk da kashe kashensu, ta hanyar yiwa mabiyansu alkawarin shiga Aljanna idan har suka yi shahada a wannan tafarkin nasu, wannan shine salon da suke bi wurin yin jihadi da yiwa matasa ingiza mai kantu ruwa domin shiga layinsu musamman ga matasan da ba su da kishin kasa da kuma sanin ciwon kai ga karancin shekaru, inda wanda ke cikin irin wannan yanayin ba abinda yake so irin taho mugama.

Irin wannan salon na jan ra’ayin mutane kan jihadi musamman a tsakanin matasa na zama kan gaba wurin tallata fahimtar dukkan masu tsattsauran ra’ayi na tsawon lokaci, domin wannan salom na zama wani taki ne mai zaburar da matasan wurin neman shahada da shiga Aljanna, a kungiyar Hasshashen Hasan Al’Sabah ya samar da wata Aljanna a cikinta akwai koramu da lanbuka da giya da mata suna waka suna rawa kamar Huril Ein, hakan nan muke gani wurin kungiyar ISIS suma suke yada wannan tunanin, hakika wani dan kungiyar ta ISIS ya bayyana a wani faifan bidiyo inda yake tabbatar da cewa yaga ‘yan matan Hurin Ein, inda ya dinga siffanta kamanninsu da kyansu bayan da aka jikkitashi a wani yaki da akayi, dan ta’addan ya tabbatar da cewa yaga Aljanna a cikinta akwai kayayyakin ado masu kyau sosai, haka nan ya sake tabbatar da cewa ya ga Manzon Allah sallallaHu AlaiHi wasallam inda ya bukace shi da cigaba da zama karkashin tutar daular musulunci saboda ita ce gaskiya abin ci.

  

Share this:

Related Fatwas