Mu’amalar masu kafirta mutane da mace
Tambaya
Mene ne matsayin mace a wurin kungiyoyin ‘yan ta’adda?
Amsa
Kungiyoyin ‘yan ta’adda suna kuntatawa mata tare ribatarsu mafi munin ribata wurin cin gajiyar bukatun duniya da manufofinta wacce ba ta da alaka da musulunci ta kowace fuska, ta yanda ake rudan matan aure musulmai da ‘yan mata kamar dai yanda akewa maza da samari, domin dai su shiga cikin wadannan kungiyoyin na su da suka sabawa sauran jama’a wurin tunani da akida da kuma jinkai na mutumtaka, kawai don fadada manufofinsu a wurare da yawa a bayan kasa, tare da yin ikirari kan kokarin tsayar da daular musulunci tare da nada kawunansu a matsayin masu yiwa musulmai wasicci a duniya, alhali sunyi hannun riga da musulunci wanda ke kasancewa addinin rangwame da sassauci da saukakawa mata, ana iya gane cewa mata sune suka fi shan wahala wurin cin zarafinsu a wurin kungiyoyin ‘yan ta’adda musamman kungiyar ISIS domin sune suka fi kowa zakewa wurin aikata munanan ayyuka da nuna cin zarafi ga wadannan kananan yaran mata.
Ita mace dai tafi shan wahala a duk wuraren da rassan kungiyar Al’ka’ida suka mamaye ko ISIS, domin kuwa akan tilasta mata rashin fita daga gidanta sai dai fa tare da muharraminta, hakanan mata na fama da takura sakamakon matsawar da ‘yan sandan mata na Hisba ke musu a duk wuraren da suka mamaye, sannan akwai wasu gungun majiya karfi da ke hukunta duk wanda ya fita daga tsarin al’ada irin na dokokinsu da ka’idojinsu.