Rashin makamar masu tsattsauran ra’...

Egypt's Dar Al-Ifta

Rashin makamar masu tsattsauran ra’ayi akan aiki da tunani mai haske

Tambaya

Mene ne sakamakon yin aiki ba tare da ilimi ko fahimta ba a cikin addini?

Amsa

Hakika malamai sunyi gargadin yin wani aiki ba tare da lura da sani a cikinsa ba, saboda hakan yana haifar da jirkicewan ma’auni na muhimman abubuwa, hakika Imamu Al’Hasan Al’Basari y ace: “ Mai yin aiki ba tare da imili ba dai kamar wanda ke tafiya ne da ya kauce hanyarsa, mai yin aiki ba tare da ilimi ba to abinda yake lalatawa yafi abinda yake gyarawa yawa”

Yana daga cikin karkatan ma’auni kan muhimman abubuwa ga wasu mutane, baiwa nafiloli muhimmanci sabanin farillai, tare da gabatar da rassa akan tushe, da baiwa ibadun daidaikun jama’a muhimmanci fiye da na ibadun mutane da yawa, da dai sauran abubuwa makamancin haka na daga cikin kaucewa, wannan yana haifar da bata lokaci da kashe karfin mutum da kuma haifar da matsaloli wurin lalata alaka tsakanin mutane, to duk wannan ya sabawa manhajin da shugabannin musulunci suka sanya, domin muna ganin yanda Imam Bukhari ya sanya babi na musamman a cikin littafinsa mai taken: “ Babin neman ilimi kafin ayi Magana akansa ko aiki da shi” sai ya kawo fadin Allah Ta’ala inda yake cewa: (Ka sani cewa babu  wani abun bauta na gaskiya sai Allah) {Muhammad:19} Manzon Allah SallaHu AlaiHi wa AliHi wasallam ya ce: (Duk wanda Allah ke nufinsa da alheri sai ya fahimtar da shi ilimin addini) Anyi ittifaki akansa, wannan hadisin yana tabbatar mana da cewa shi fahimta a addini da kuma aiki da fahimta yana ginuwa ne bisa ingantaccen tsari wanda hakan yafi yin aiki kai tsaye, domin abu mafifici shine baiwa ingantaccen fahimta muhimmanci sannan daga baya kuma aiki da hakan bisa gurbinsa.

Hakika musulunci ya tabbatar da sunnar bin matakai da lizimtar hikima wurin bin lamura, wanda hakan ya bayyana a yanayin shar’anta lamura mabanbanta kamar dai haramta giya wanda hakan bai tabbata ba sai bayan matakai har guda hudu, da kuma tabbatar da yin jihadi wanda sai an samu mutum daya da ke zama matsayin mutum biyu har zuwa goma, da dai sauransu wanda ke bayyana muhimmancin fahimtar hakikanin rayuwar mutane da halayyarsu ko kuma a fagen shar’anta hukunce hukunce ne.

Share this:

Related Fatwas