Hadisin “wasu jama’a daga cikin al’...

Egypt's Dar Al-Ifta

Hadisin “wasu jama’a daga cikin al’ummata ba za su gushe ba su na masu tsayawa akan tabbatar da gaskiya ”

Tambaya

Da yawan masu tsattsauran ra’ayi suna jingina da Hadisin nan na “wasu jama’a daga cikin al’ummata ba za su gushe ba su na masu tsayawa akan tabbatar da gaskiya” shin wannan Hadisin ingantacce ne? kuma mene ne ma’anarsa?

Amsa

Wannan yana daga cikin Hadisan da masu kafirta mutane suke kafa hujja da shi domin lullube gaskiya, tare da nunawa mutane jiji da kai, sakamkon mummunan fahimtarsu, da kuma fita daga layin fahimtar shari’a da shugabanni suka tafi akai dangane da fahimtar Hadisan da suka yi magana akan wannan matsayin.

Babu wani kura akan ingancin wannan Hadisin, ya zo ne a siyakin bayar da labari akan sunnar rayuwa da sai ta faru babu makawa, bai kasance abun assasawa ba, ko siffanta wasu mutane ko kungiya, ba hakkin wasu mutane ko wata kungiya bane kebance wannan siffar gare su, Annabi SallaHu AlaiHi wasallam baya nufin fayya cesu, kawai dai abin nufi da hakan shi ne muyi kokarin tabbatar da wadannan siffofin a kawukanmu,  ballantana kuma barnannaki da ke faruwa idan kowani mai ikirari yayi ikirarin abin da babu tare da shi, daga haka sai mutane suka karkasu zuwa kashi-kashi da kungiyoyi daban daban inda kowani bangare zai rinka kira ga tasa fahimtar da manhajinsa, kuma ma’anar wannan Hadisin zai iya zama kowace kungiya tana karkasuwa tsakanin nau’ukan muminai daga cikinsu inda wasu sadaukai ne masu yaki, wasu kuma fakihai ne, daga cikinsu kuma akwai malaman Hadisi, daga cikinsu akwai masu zuhudu, da kuma masu umurni da kyawawan ayyuka da hani akan abun ki, duk dai daga cikin akwai ma’abota aikata wasu alhairan na daban, ba dole bane kuma su kasance a tattare wuri daya, kila ma su kasance a rarrabe a yankuna daban daban na duniya, abin da ake nufi da wannan Hadisin shi ne kwadaitar da mu kan mu kasance ma’abota aikata alheri, kuma ma’abota bin gaskiya ba wai killaceta a garemu ba.

Share this:

Related Fatwas