Matsa kaimi wurin yaki da tsattsaur...

Egypt's Dar Al-Ifta

Matsa kaimi wurin yaki da tsattsauran ra’ayi

Tambaya

Ta yaya wadanda alhakin ya rataya a wuyansu za su iya matsa kaimi wurin kalubalantar ayyukan tsattsauran ra’ayi da ta’addanci? 

Amsa

Babu makawa fa sai dukkan cibiyoyin da alhakin yaki da ta’addanci ya ratayu a wuyansu su riske cewa aikinsu fa ya shafi addini da kuma kishin kasa, domin illar da ta’addanci yake haifarwa ba wai ya takaita ne cikin gida da kasashen waje ne kawai ba, ai illarsa yakan shafi zaman lafiyan yakuna da kuma kasashe gaba daya, wannan hatsarin yana zuwa ne domin wancakalarwa da rashin daukan matakan da su ka dace a tsawon lokaci mai nisa domin yakar wannan tunanin, don haka wadancan cibiyoyin – musamman na addini- su cigaba da yin kokarin yin tattali na bayar da horo ga wasu zaratan mutane da malamai da masu kira zuwa ga Allah a matakin kasashen duniya domin kalubalantar wannan lamari a matakin kasashen duniya, domin wadannan da suka samu horon za su iya kalubalantar tunanin ta’addanci a ko’ina cikin kasashen duniya, wanda tasirin hakan zai bayyana sosai a wurin wannan yaki.

Sannan ya kamata cibiyoyin da suke wannan aiki su kebance wani shiri na musamman domin bayar da horo na kalubalantar tunanunnka da tsattsauran ra’ayi da sanin hanyoyin kare kai daga hakan.

A cikin shirin da wadannan cibiyoyin za su gabatar akwai samar da tawagogi a kasashen waje da za su yi aiki tukuru wurin warware tunani na ta’addanci da kuma samun lagon kalubalantarsu.

Hakanan su yi kokari wurin fadada dandalolinsu a fagen duniyar yanar gizo – koda yaushe – kamar dai samar da shafuka na musamman da harshen Larabci da kuma sauran harsuna domin yakar tsattsauran ra’ayi da ta’addanci.

Share this:

Related Fatwas