dalilan yaduwar ta’addanci

Egypt's Dar Al-Ifta

dalilan yaduwar ta’addanci

Tambaya

Shin ta’addanci sabon abu ne? mene ne dalilin yaduwar ta’addanci a wannan lokacin da muke ciki?

Amsa

Shi ta’addanci dai wani abu ne da ya dade idan akayi la’akari da samuwar dan adam, alaka tsakanin ta’addanci da samuwar dan adam tana siffantuwa ne da lizimtar juna kwarai da gaske, yin amfani da tsauri tare da ayyukan laifuffuka domin tayar da zaune tsaye da firgici a zukatan al’umma na kasancewa daya ne daga cikin hanyoyin da mutum kan yi domin biyan bukatunsa na kashin kai, da kuma cika burinsa, don haka ne ma za mu ga wasu hanyoyi sababbi da munana suna taka rawa sosai wurin yada ta’addanci a cikin al’umma, duk hakan na kasancewa ne sakamakon yanda shi mai tsattsauran ra’ayi ke yawan samun kalubale tsakaninsa da al’umma da ma mutanen duniya baki daya, sai muga yana karkata zuwa ga fassara abubuwan a kan fahimta irin ta sa shi kadai, tare da yiwa waninsa kallon abokin gabansa ta kowani fuska.

Irin wadannan ayyukan da suke yamutsa hazo sune suke tabbatar da tsarin gabatar da Magana mai dauke da tsattsauran ra’ayi wanda ke aminta da karbar zafafan lamura da kuma ta’addanci a matsayin wani abu ne mai iya yiwuwa, ko kuma ya dace a shari’ance, wata kila hakan daga karshe – Amma ba dole bane – zai iya kaiwa zuwa ga tunkuda mutum ga aikata ta’addanci ko goya masa baya.

A bisa kowani hali dai, hanyoyi mabanbanta da ake bi domin fassara zahirin tsattsauran ra’ayi a karkace to zahirin lamarin ba zai bayyana ba sai an hangeshi ta dukkanin hanyoyi masu yiwuwa ta ciki da waje a lokaci guda, saboda shi tsattsauran ra’ayi a hakikaninsa ya kasance abu ne mafi hauhawa da kuma sarkakiya wurin fahimtarsa ta hanyar kadaici mai nesa daga sauran abubuwa na waje ko akasin haka.

Share this:

Related Fatwas