Tsattsauran ra’ayin wurin Magana

Egypt's Dar Al-Ifta

Tsattsauran ra’ayin wurin Magana

Tambaya

Mene ne tsattsauran ra’ayin Magana? Kuma menene alakar da ke tsakaninsa da waninsa cikin nau’ukan tsattsauran ra’ayi?

Amsa

Shi zafafa kalamai na zance ko tsattsauran ra’ayi yana kasancewa mataki ne na biyu daga cikin matakan tsattsauran ra’ayi, daga nan ne mai tsattsauran ra’ayi ya ke tsinkaya zuwa ga rungumar mummunar tunani ta hanyar yin amanna da ita da fara aiwatar da ita ta hanyar furta kalamai, daga haka sai sai aga mai wannan fahimta yana yawan furta munanan kalamai da bakinsa ba wai a aikace ba.

Babu shakka lallai tsattsauaran ra’ayi na zancen baka shi ne dan jagoran mutum zuwa ga tsattsauran ra’ayi na aikace da yin ta’addanci ta hanyoyi da daman gaske, alaka tsakanin yanayi na farko (tsattsauran ra’ayi na zancen baka) da kuma na karshe (tsattsauran ra’ayi na aikace), sun sha banban sosai da tsattsauran ra’ayi na zancen baka da kuma na aikatawa, fuskar sabanin da ke tsakaninsu shi ne yiwuwar hauhawan da tsinkayar abubuwan biyu da kuma matakansu, yiwuwar tsinkayar mai tsattsauran ra’ayin zuwa aikata zafafan ayyuka yana da karanci sosai akan wadanda su aikinsu shi ne furta kalamai tsaurara na zancen baka ko kuma aikata ayyuka zafafa masu tsauri.

Wata kila sakamakon hakan yana komawa ne zuwa ga daya daga cikin ayyukan ta’addanci, ko nau’ukansa, shi mai tsattsauran ra’ayi a lokacin da yake furta kalamansa masu tsauri ta hanyar kamantawa ko bayyanawa da tattaunawa, to wannan shi ke bayyana cewa ya fara shiga matakin aikata ta’addanci, duk da cewa fa bai shiga ainihin aikata mafi muni daga cikinsa ba, don haka ciruwa tsakanin matakai biyun nan – koda kuwa hakan bai zama dole ba – to kamar dai tasowa ne daga matakin yin tunani akan abu da kuma aikata abun, sai dai fa yiwuwan hakan abu ne mai sauki sosai da sosai, kuma abu ne mai iya yiwuwa, domin wasu mutanen ma sun sauke tsattsauran ra’ayi na zancen baka a amatsayin ta’addanci da tsattsauran ra’ayi mai zafi.

Share this:

Related Fatwas