Rauni wurin sanin ilimi na shari’a

Egypt's Dar Al-Ifta

Rauni wurin sanin ilimi na shari’a

Tambaya

Mene ne gudunmawar da runin ilimi na shari’a ke bayarwa wurin samar da kwakwalwa irin na mai kafirta mutane?

Amsa

Shi jahilci wani yanayi ne wanda ya dace da yaduwar ta’a’ddanci a farfajiyarsa, saboda ra’ayuyyuka na ta’addanci a fafaki suke, domin suna dogara ne akan dalilai na son zuciya, da yiwa nassosin addini fassara sama –sama ko na fafaki, don haka irin ayyukan bayar da horo ga mabiya na yawaita ne ga wadanda suke da karamin sani a addini, saboda rashin sanin yanda za su iya warware maganganu  na ta’addanci, da iya lakantar yanda ake warwareshi da raunin da ke tattare da shi, so da yawa irin haka na bayyana ne a wurin kididdige gwargwadon sani da ilmin da wadancan mayakan suke da shi a fagen addini.

Saboda haka ne ma masu goya wa lamuran masu tsattsauran ra’ayi baya suke kokarin gina wani sabon madogara na fahimta wanda zai taimaka wurin gina fahimtarsu, saboda haka abu na farko da mutum zai ci karo da shi idan ya fara karanta sakamakon fahimtar masu tsattsauran ra’ayi ko bibiyan abubuwan da suke yadawa shi ne tarin wadansu ra’ayuyyuka da suke taimakawa wurin gida manhajinsu na ta’addanci, sai muga suna bayyana ma’anar “Gidan kafirci da gidan musulunci” da irin ta su fahimtar kamar yanda yake a wurin Sayyid Khudub da waninsa, domin tabbatar da cewa al’ummarsa jahila ce, kuma kasar da yake rayuwa a ciki kasa ce ta kafirci ba ta musulunci ba, ana kiran irin wadannan kasashen da “Alhakimiyya” wato ta yaya hukunci a kasa zai kasance na musulunci, domin a yarda da cewa dukkan sassan gwamnati kafirai ne, ko kuma duk wanda yake taimakawa gwamnati wurin aiwatar da ayyukanta, sannan kuma sai koyar da jihadi da kuma hanyar aiwatar da shi, domin karfafa kashe fararen hula da musulmai da sauran mutane mabiya addinai da dama, to a irin haka ne sabon ra’ayin da aka dasa a cikin zukatan irin wadanda suka shiga cikin kungiyoyin nan sai su karkata zuwa ga aikata ta’addanci.

Share this:

Related Fatwas