Bayar da fatawa da da’awa

Egypt's Dar Al-Ifta

Bayar da fatawa da da’awa

Tambaya

Mene ne bambancin da yake tsakanin bayar da fatawa da kuma yin da’awa?

Amsa

Bambancin da yake tsakanin Da’awa da bayar da fatawa yana bayyana ne ta fuskar aikin da shi mai da’awar yake aikatawa na shiryatar da mutane da kuma isar da sakon da tsari ko salo na zance ga dukkanin mutane wurin sanar da su ginshikan addini da mua’amala da kyawawan dabi’u, amma shi bayar da fatawa aiki ne mai tsaurin gaske na musamman wanda ya kasancewa a kan wasu abubuwa da suka faru  da kuma wasu yanayi bayyanannu da ake neman sanin hukuncin shari’a dangane da su, hakika akan iya samun mai bayar da fatawa ya gudanar da aikin mai yin da’awa da yin da’awa zuwa ga Allah, amma mai da’awa ba ya iya aikin mai fatawa ko yin fatawa a tsakanin mutane, sai dai fa idan ya samu ilimin da zai ba shi daman yin fatawar, to anan zai iya aikin bayar da fatawa ga duk wanda ya tambaye shi, saboda aikin fatawa aiki ne wanda ya kasance karkashin kwarewa da ijitihadi bisa wasu sharudda bayyanannu, haka nan wanda ya kware wurin yin wa’azi shi ma, hakika wanda ya samu ilimin bayar da fatawa ya zama yana da tawaya a wurin yin bayani a gaban mutane, kamar dai yanda ake samun mujadala da yin gaba da gaba wanda yake mai kyau sobada neman gaskiya, to aikin bayar da fatawa ba ya aiki a irin wannan bigire, saboda duk mai tambaya idan zai yi tambaya ba ya bukatar yin jayayya ko fito na fito da hujjoji, abin da yake bukata kawai shi ne neman bayani don fahimta ga hukunce hukunce na shari’a, duka su biyun suna yin tarayya a wurin kulawa da halin da mai tambaya yake ciki ko wanda ake yi wa da’awar, bisa yanayin zamani da wuri da abubuwan da suke caccanzawa.

Mai da’awa yana himmatuwa da yin wa’azi ne domin rausasa zukata da cusa tsoron Allah a cikn zukatan mutane tare da zaburar da zukatansu, amma shi mai bayar da fatawa yana himmatuwa ne da gyara tsarin ibada ga mutane da inganta mu’amalolinsu da yin bayani akan hukunce hukunce na shari’a, aikinsa ba ya rataya da rausasa zukatan mutane ko wani aiki na wa’azi.

Share this:

Related Fatwas