Fikihu da shari’a

Egypt's Dar Al-Ifta

Fikihu da shari’a

Tambaya

Mene ne bambancin fikihu da shari’a?

Amsa

Lallai bambancin da yake tsakanin fikihu da shari’a yana bayyana ne ta fuskar cewa: ita shari’a matattara ce ta ka’idoji da usuli na bai daya wanda aka tsamo daga littafin Allah da sunnar Annabi SallallaHu AlaiHi wasallam, don haka sun shafi hukunce- hukunce na ayyuka da na akida da halayya da mu’amala da kuma tsara hakan a tsakanin mutane a sashe da sashe, da kuma tsakanin mutane da wadanda suka saba musu, amma shi fikihu ya kunshi hukunce- hukunce ne na shari’a a tsawon lokaci, daga cikin irin wannan hukunce- hukuncen akwai tabbatattu kadai daga cikinsu, wanda haka shi ne aikin da shugabanni mujtahidai suka yi tare da yin istinbadin hukunce hukunce daga ciki akwai mai canzawa da mai sabunta kansa ta fuskar abubuwa da halaye da kuma zamani da wuri.

Ita shari’a ta bai daya tabbatacciya ce ba ta canzawa, shi kuma fikihu kebantacce ne yana canzawa ana kuma gina shi akan ijitihadi da tunani, haka nan shari’a takan luzumci kowani Musulmi ne sau da kafa idan har sharudda na taklifanci sun hau kansa, don haka shi abin yi wa lizimta ne da dukkan wani al’amari na shari’a na daga hukunce hukunce da akida da dabi’u da halayya, amma shi Musulmi ana yi masa rangwame ya zabi daya daga cikin mazhabobin fikihu da yake so.

Haka nan ita shari’a ingantacciya ce ga kowani zamani da wuri, amma shi fikihu ijitihadi ne, zai iya kasancewa ya yi daidai da zamani amma ba ya kasancewa daidai da wani zamani daban, ko kuma ya kasance ingantacce ne ga wani wuri da al’umma ta musamman ba ta kowa da kowa ba, wannan bambancin na ma’ananonin ilimi ne, idan ba haka ba to fikihu wani sashe ne ko yanki ne na shari’a, saboda fahimta shari’a da amfaninta na karkashin ijitihadi ne da yin aiki da shi.

Share this:

Related Fatwas