Yin misila da gawarwaki
Tambaya
Shin ya halasta ayi misila da gawarwaki?
Amsa
Bai halasta ba a shari’ance a yi misila da gawarwaki, hakika shari’ar Musulunci ta zo ne da kyawawan ayyuka da dabi’u a dukkan halaye domin yin bayanin ainihin addinin Musulunci da fayya ce hakikaninsa wurin girmama dan adam da nuna masa jin kai saboda girmamawa daga Allah Ta’ala: (Hakika mun girmama ‘yan adam inda muka daukesu a kan tudu da cikin ruwa kuma muka azrutasu da abubuwa masu dadi sannan kuma muka daukakasu akan mafi yawa daga cikin abin da muka halitta matukar daukakawa) [Isra’a:70].
Hakika Annabi SallallaHu AlaiHi Wassalam ya yi hani daga yin misila wa gawarwaki, inda ya ce: (kada ku yi misila da dan adam, ko kuma da dabba, kuma kada ku yi zalunci kada ku wuce gona da iri) [Baihaki], masana ilimi sun ce: abin nufi da fadin Manzon Allah SallallaHu AlaiHi Wassalam :
“Na ka da ku yi misila da dan adam ko da dabba” yana fa’aidantar da hani ne akan yin misila baki daya, kuma wannan hanin akan misila gamamme ne a cikin dukkan yanayi, hakika hanin Annabi kan yin misila yazo cikin hadisai masu yawa wadanda suke bayyana wannan hanin na Annabi SallallaHu AlaiHi Wassalam kan wannan mummunan aikin.
Arabic
Englsh
French
Deutsch
Urdu
Pashto
Swahili
