Tasirin yada jita- jita a cikin al’...

Egypt's Dar Al-Ifta

Tasirin yada jita- jita a cikin al’umma

Tambaya

Mene ne wajibi akan musulmi dangane da jita- jitan da ake yawan yadawa a kusa da shi?

Amsa

Musulunci ya toshe kafofin yada jita-jita, ta inda ya dorawa musulmai nauyin tabbatar da labaru kafin yanke hukunci akansu, sannan ya yi umurni da mayar da lamura zuwa ga ahalinsu, tare da sanin hukuncin hakan kafin yadawa da yin tsokaci akansu, Allah Mai girma ya ce: (Ya ku wadanda kuka yi Imani idan wani fasiki yazo muku da wani labari to ku yi bincike a kai domin kar ku yiwa wasu mutune hukunci a bisa rashin sani don gudun kar kuzo kuna nadamar abin da kuka yi) [Alhujurat:6]

Hakana nan Musulunci ya hana sauraron jita- jita tare da yadawa, kuma Allah Mai girma ya zargi wadanda suke jiyar da mutane jita- jita tare da yadawa tsakanin mutane domin tayar da fitina, Allah Mai girma ya ce: (Da ace su “munafukai” za su fita jihadi tare daku to ba abin da za su kara muku sai sharri da barna kuma da sunyi gaggawa wurin yada barna a tsakaninku su na neman tayar da fitina kuma daga cikinku akwai masu biye musu wurin son yada fitina Allah shine mafi sanin azzalaumai) [Tauba:47]

Share this:

Related Fatwas