Zaman addu’an kwanaki Arba’in da na shekara ga mamaci.
Tambaya
Mene ne hukuncin yin addu’ar kwanaki arba’in ko na shekara ga mamaci?
Amsa
Jumhorin malaman fikihu sun tafi akan cewa kwanakin zaman ta’aziyya da karban gaisuwar rasuwa kwanaki uku ne kacal, kuma ta’aziyya bayan kwanakin uku abin karhantawa ne, sai dai fa ga wanda baya nan a lokacin sai daga baya ya dawo ya zo, ko kuma ga wanda bai san da rasuwar ba sai bayan shudewar wani lokaci, saboda hakan yana sake dawo da bakin cikin rabuwa da wanda aka rasa ne, tare da dorawa ‘yan’uwan mamaci abin da ba za su iya ba.
A shari’ance babu hani kan a taru domin aikata wani akin lada domin shi mamacin ya amfana, kamar dai ciyar da abinci, da karanta Alkur’ani, shin a cikan kwanaki Arba’in ne ko cikan shekara.