Neman biyan bukata da Annabi (Salla...

Egypt's Dar Al-Ifta

Neman biyan bukata da Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) da Alil Baiti da kuma Ka’aba.

Tambaya

Mene ne hukuncin mutum ya yi fatan wani ya zama sanadin cikan burinsa ta hanyar tarajji da Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) da iyalan gidansa da Ka’aba?

Amsa

Shi dai tarajji ko fatan abu ko karfafa zance da hadawa da darajan Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) ko da waninsa kamar dai mutum ya ce: Don darajan Annabi – ko Don girman Ka’aba… wanda ba ya nufin rantsuwa da su a zahiri to ya halasta a shari’ance kuma babu laifi akan haka a wurin jumhor din malaman fikihu, bai halasta a hana yin hakan ba bisa la’akari da zahirin dalilai na haramta yin rantsuwa da wanin Allah, to bashi a cikin wannan babin, wanda ya kasance ya zo cikin zancen Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) da maganar sahabbai masu girma, an karbo daga Abu Huraira – Allah ya kara masa yarda – ya ce: Wani mutum ya zo wurin Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) sai ya ce: Ya Manzon Allah, wace sadaka ce mafi girman lada? Sai Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) ya ce masa: “Ina gama ka da darajan mahaifinka lallai sai kun bayyana shi, kayi sadaka kana mai tsananin lafiyar dabukatar abin da ka bayar kuma kana tsoron talauci da son wanzuwa”.

Imam Bukhari da Imam Muslim sun ruwaito cewa matar Abubakar   Siddik – Allah ya yarda da su – tace masa: (A a ba haka bane tauraruwar idanu na, yanzu tafi baya yawa da ribi uku) tana nufin abincin bakinsa.

Allah Madaukakain Sarki mafi sani.

Share this:

Related Fatwas