Zana hutuna a riguna da wasu abubuw...

Egypt's Dar Al-Ifta

Zana hutuna a riguna da wasu abubuwa na daban

Tambaya

Mene ne hukuncin zana wasu hotuna akan tufafi ko bango ko wani abu makamancin haka?

Amsa

Babu laifi a yi zane a irin wadannan abubuwa da aka ambata matukar dai hotunan ba su shafi abubuwan da ba su halasta a bayyanasu ba ko a zanasu, kamar a ce tsaraici, ko wani aiki mare kyau, ko kuma ya zama ingiza mai kantu ruwa ne akan sabawa umurnin da shari’a ta gindaya, ko kuma zanen ya kunshi yin fito na fito da shugaba (dokokin kasa ko shugaba ko daula), idan hotunan ko zanukan sun shafi haka to sun haramta, ba wai kasancewarta hoto ba, sai dai fa kawai ta dalilin wani abu da hoton ya kunsa, to wannan shi ne wanda ya kunshi haramtattun abubuwa, yana daga cikin abubuwan da suke karfafa hakan halasta hoto da zane a rufi ko gini da makamantar haka abin da ya zo daga Abu Dalhat – Allah ya kara masa yarda – shi ne cewa  Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) ya ce: (Mala’iku ba sa shiga gidan da akwai hoto a cikinsa) Busrun ya ce: sai Zaidu bin Khalid ya yi rashin lafiya sai muka je gaisheshi, a ya yin da muke gidansa sai muka ga wani labule a jikinsa akwai zane, sai na cewa UbaidulLah Al-khaulany: shin bai mana Magana akan zane zane ba?  Sai ya ce ai ya ce ne: “sai dai zane a tufa” shin baka jishi bane?  Sai ya ce: a a, sai ya ce hakane, hakika ya ambaci haka. Anyi ittifaki akansa.

Share this:

Related Fatwas