Tsintuwar da ma’aikacin hotel zai y...

Egypt's Dar Al-Ifta

Tsintuwar da ma’aikacin hotel zai yi

Tambaya

Mene ne hukuncin tsintuwar da ma’aikacin hotel ya yi?

Amsa

Kowa ya san cewa kiyaye dukiya da rashin lalata ta, ko salwantar da ita daya ne daga cikin manyan manufofin shari’ar Musulunci; sai dai mai ita yana iya rasawa, waninsa ya tsinta, wannan shi ne ake kira da “tsintuwa”, abin da yake tabbatacce a cikin shari’a shi ne idan dukiyar mutum ta fadi, fadin ba ya sanya wannan dukiyar ta fita daga karkashin mallakarsa, shari’a ta halatta a dauki kudi ko dukiyar da aka tsinta ne domin a isar da ita ga mai ita, hanyoyin isarwar kuwa ta sha bamban daidai da bambancin da yake cikin tsare- tsare da al’adu, a wannan zamanin ana yin haka ne ta hanyar mika ta ga ofisoshin ‘yan sanda, a duk sanda aka kasa isa zuwa ga mai ita, shi kuma ma’aikacin hotel idan ya yi tsintuwa a cikin dakunan da yake aiki, sawa’un abin da ya tsinta din babba ne da yake da kima, ko ba shi da wata kima, to dole ne ya mika wa hukumar da take gudanar da hotel din, domin ta dauki matakan isar da ita ga mai ita.

Share this:

Related Fatwas