Karanta suratu “Yaseen” da niyyar s...

Egypt's Dar Al-Ifta

Karanta suratu “Yaseen” da niyyar samun biyan bukata.

Tambaya

Mene ne hukuncin karanta suratu “Yaseen” da niyyar samun biyan bukata da kuma samun saukin al’amura?

Amsa

Shi karanta Alkur’ani Maigirma yana daga cikin lamuran da suke jawowa mai yi yawan albarka da lada da sakamako daga Allah Maigrima da Buwaya, yana daga cikin surorin da falalar karanta ta yazo daga hadisai masu yawa suratu “Yaseen” an karbo daga Mu’ukal bin Yasar Allah ya kara masa yarda cewa lallai Manzon Allah SallallaHu AlaiHi wa AliHi wasallam yace: (Suratu Yaseen zuciyar Alkur’ani ce, wani mutum bai karanta ta ba da niyyar niman yardan Allah da neman lahira face an gafarta masa, ku karanta ta ga mamatanku) Ahmad.

Karanta suratu “Yaseen” na da falala maigirma, kuma mai karanta ta yana da lada mai yawa daga Allah Azza wa Jallah, hakika wani sashe na malamai sun tabbatar da halascin karanta suratu Yaseen da niyyar niman biyan bukata da kuma yayewar bakin ciki, kamar dai niman wadata a cikin arziki da samun daman biyan bukata da samun saukin lamura ko kuma makamancin haka cikin ayyukan alheri, lallai fa wanda ya karanta suratu Yaseen yana mai yakinin cewa Allah Maigirma da Buwaya zai biya masa bukatarsa saboda albarkacin karanta Alkur’ani da kuma suratu Yaseen to da yardan Allah bukatarsa za ta biya.

Share this:

Related Fatwas