Yin majalisan zikiri a masallatai

Egypt's Dar Al-Ifta

Yin majalisan zikiri a masallatai

Tambaya

Mene ne hukuncin yin majalisan zikiri a masallatai?

Amsa

Gabatar da majalisan zikiri da sallatin shugabanmu manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) a masallatai, da ma wasun masallatai –bayan amincewar hukumomin da abin ya shafa- daya ne daga cikin halattattun ibada da shari’a ta amince da su, kuma hakan ya yi daidai da Alkur’ani da Sunnah da karantarwar magabata na gari, da malaman al’umma da suka biyo bayansu, kuma akan haka ne ayyukan Musulmai a dukan zamunna da garuruwa, ba kuma tare da an sami inkari ba, matukar an kiyaye ladubban shari’a da na tsare- tsaren gudanarwa a wadannan wuraren.

Yin zikiri a bayyane a cikin ire- iren wadannan majalisai tare da kulawa da abubuwan da suka gabata, abu ne da ya halatta, ta yanda zai zama a yanayin da ba zai kawo cikas ga masu sallah da masu zikiri da masu karanta littafin Allah Madaukakin Sarki; saboda bin karantarwar Annabi mai girma (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) a inda yake cewa: (Kada wasu daga cikinku su daga murya wa wasu a wajen karanta Alkur’ani) Imam Malik ya ruwaito a Muwadda, da Imam Ahmad a cikin al- Musnad.

Share this:

Related Fatwas