Yin magana cikin al’amurran ilimin likitanci ba tare da ilimi ba.
Tambaya
Mene ne hukuncin Yin magana cikin al’amurran ilimin likitanci ba tare da ilimi ba?
Amsa
Fada wa mara lafiya magani aiki ne na likita da yake kulawa da shi, sam bai halatta wanin likita ya yi gigin yin Magana akan al’amurran da suka shafi aikin likitanci, ko bayyana magani ga mara lafiya ba, lallai Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya gargadi duk mutumin da ya sanya rigar likitanci alhali ba likita ba ne, ya kuma rubuta wa waninsa magani, ya bayyana cewa duk mai yin haka shi ne zai dauki alhakin abubuwan da za su je su dawo sakamakon aika- aikarsa, kyawon niyyarsa ba zai cece shi ba, (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Duk wanda ya sanya rigar likitanci, alhali shi ba likita ba ne kafin lokacin, to shi zai lamunci abin da zai je ya dawo) [Abu Dawud], abin da ake nufi da sanya rigar likitanci shi ne ya shiga aikin bayar da magani cikin jahilci da rashin sani, hakan yana nufin cewa, ya shiga ciki ne alhalin bas hi da ilimin abin.
Lallai ya kamata duk mai hankali ya nesanci mika lafiyar jikinsa a hannun kowane gaja, wanda bai san komai ba, domin yin rikon sakainar kasha da lafiya, da cutar da jiki nau’i ne daga cikin nau’o’in barna a bayan kasa, ya kuma ci karo karara da irin yanda Musulunci yake kula da bai wa rayuwar dan Adam kariya, da haramta yi masa kowane irin ta’addanci.