Maganar cewa: “Kasar Misra kasa ce ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Maganar cewa: “Kasar Misra kasa ce mai albarka, ita ce uwar kasashe”

Tambaya

Mene ne ingancin maganar cewa: “Kasar Misra kasa ce mai albarka, ita ce uwar kasashe”?

Amsa

An sanya wa Misra sunan “Uwar Duniya”, ko “Uwar kasashe, madogara bayi”; wannan suna ne da Annabin Allah Nuhu (AlaiHis Salam) ya sanya mata; Ibn Abdulhakam a cikin littafin “Futuhu Misra wal Maghrib” shafi: 27 ya kawo cewa: daga Abdullahi Bn Abbas (Allah ya kara yarda da su) ya ce: Lallai Annabi Nuhu (AlaiHis Salam) ya fada wa dansa, lokacin da ya amsa kiransa cewa: (Ya Ubangiji Allah, lallai ya amsa kirata, ka yi masa albarka, shi da zuriyarsa, ka zaunar da su a gari mai albarka, wadda take ita ce Uwar garuruwa, madogara bayi, wadda koginta ya fi dukan kogunan duniya, ka sanya mafificin albarka a cikinta, ka hore masa shi da dansa kasa, ka sa ta yi masu sauki, ka kuma karfafe su akanta), wannan labara ne da malamai masu yawa suka kawo shi a cikin litattafansu, suka kafa hujja da shi akan daraja da matsayin Misra, a cikin malaman akwai: al- Hafiz al- Kindiy a cikin littafin “Fadha’ilu Misral Mahrusa”, da shahararren malamin tarihin nan al- Bakriy a cikin littafin “al- Masalik wal Mamalik”, da shahararren malamin tarihin nan Ibn Taghriy Bardiy a cikin littafin “Annujuz Zahira”, da al- Hafiz al- Suyudiy a cikin littafin “Husnul Muhadhara”, da babban malamin nan al- Maqriyziy a cikin littafin “al- Mawa’iz wal I’itibar”, da sauransu.

Share this:

Related Fatwas