Bukukuwan tunawa da Isra’i da Mi’ir...

Egypt's Dar Al-Ifta

Bukukuwan tunawa da Isra’i da Mi’iraji.

Tambaya

Mene ne hakikanin bikin tunawa da Isra’i da Mi’raji da ake yi a duk ranar Ashirin da bakwai na watan Rajab?

Amsa

Abin da aka sani dai daga cikin zantuttukan malamai a baya da yanzu da kuma abin da musulmai ke aikatawa shi ne shi Isra’i da Mi’iraji ya faru ne a daren Ashirin da bakwai na watan Rajab. Don haka bikin da musulmai sukeyi domin tunawa da wannan lamari na tarihi na nuna nau’ukan biyayya da neman kusanci ne ga Allah, kuma hakan  abu ne wanda aka shar’anta kuma akaso ayi, domin hakan yana nuna farin ciki ne ga Annabi SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam da kuma girmama matsayinsa, amma maganganun da ake yi na haramtawa musulmai yin murna da bukukuwan tunawa da zagayowar wannan lamari mai girma, to maganganu ne marasa tushe da basu da makama, kuma bai halasta a dauki wadancan maganganun ba ko a kallesu.

Share this:

Related Fatwas