Addu’a bayan tahiyar karshe a salla...

Egypt's Dar Al-Ifta

Addu’a bayan tahiyar karshe a sallah

Tambaya

Mene ne hukuncin addu’a bayan tahiyar karshe a sallah?

Amsa

Addu’a bayan tahyar karshe sunna ce da ta zo daga Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam); amma mustahabi ne ba wajibi ba, mutum yana da daman ya roki duk abin da yake so a al’amurran duniya da lahira, yana kuma da daman ya yi addu’a da addu’o’in da aka ruwaito, kaman yanda yake da daman yin kowace addu’a, a cikin addu’o’in da aka ruwaito akwai wanda Bukhari da Muslim suka ruwaito ta hanyar Sayyida A’isha (Allah ya kara yarda da ita), cewa lallai Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yana addu’a a cikin sallah yana cewa: “Ya Allah ina neman tsarinka ga barin azabar kabari, ina neman tsarinka ga barin fitinar mai shafaffen albarka Dujal, ina neman tsarinka ga barin fitinar rayuwa da ta mutuwa, ya Allah ina neman tsarinka ga barin aikata zunbi da asara”.

Share this:

Related Fatwas