Yin wa’azi kafin gabatar da sallar ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Yin wa’azi kafin gabatar da sallar jana’iza da lokacin rufe gawa

Tambaya

Mene ne hukuncin yin wa’azi kafin gabatar da sallar jana’iza da lokacin rufe gawa?

Amsa

Gabatar da huduba ko wa’azi a lokacin da ake jiran kawo jana’iza don yi mata sallah mustahabi ne, haka ma da a makabarta lokacin rufe gawa; lallai akwai Hadisai ingantattu da suka zo daga Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) da suka bayyana cewa lallai (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yana yi wa sahabbansa wa’azi bayan rufe gawa da kafinsa; a cikin Hadisan akwai Hadisin Sayyiduna Aliyu (KarramalLahu wajhahu), wanda Bukhari da Muslim suka ruwaito, ya ce: Wata rana muna wurin wata jana’iza a Baki’ul Garkadi, sai Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya zo, ya zauna, muka zauna a gefensa, yana tare da wata sanda mai lankwasa, sai ya dukar da kansa, yana zana wani zane da sandarsa, sannan ya ce: (Babu wani daga cikinku, ko babu wani rai mai numfashi face an riga an rubuta masa wurinsa a aljanna da wuta, face kuma an rubuta masa tababbe ne, shi ko mai rabo) sai wani mutum ya ce: ya Manzon Allah, shin ba ma dogara da abin da aka rubuta mana mu bar aiki ba? duk wanda yake cikin masu rabo daga cikinmu sai bi hanyar aikata aiki irin na masu rabo, wanda kuma yake cikin tababbu a cikinmu, zai bi hanyar aikata aiki irin na tababbu, sai ya ce: (Su masu rabo za su bi tafarkin aikata aikin masu rabo, su kuma tababbu, za su bi tafarkin aikata ayyuka irin na tababbu) sannan ya karanta: (Shi kuwa wanda ya bayar, ya kuma ji tsoron Allah, ya kuma gasgata kyawawan abubuwa..) [al- Lail: 5- 6].

 

Share this:

Related Fatwas