Yiwa Annabi SallallaHu AlaiHi wa Sa...

Egypt's Dar Al-Ifta

Yiwa Annabi SallallaHu AlaiHi wa Sallam salati a lokacin sallah.

Tambaya

Mene ne hukuncin yiwa Annabi SallallaHu AlaiHi wa Sallam salati a lokacin sallah?

Amsa

Yiwa shugabanmu Manzon Allah SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam salati alokacin da mutum ya ji an yi ko ya karanta sunansa a lokacin sallah abu ne da a kasa a shari’ance, hakan yana da falala mai girma, hakika Allah Ta’ala ya kwadaitar damu akan haka, inda ya ce: (Lallai Allah da mala’ikunsa suna yiwa Annabi salati ya ku wadanda kuka yi Imani kuyi masa salati sannan kuyi kuna masu mika wuya akan haka)[Al’ahzab:56] hakika jumhorin malamai sun tafi akan duk wanda yaji sunan Annabi SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam a lokacin sallah ko ya karanta wata aya da akwai sunansa  SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam: to yayi masa salati, sallarsa ba ta baci ba, saboda yi masa salati abin umurni dashi ne a duk sanda aka ambaci sunansa, saboda hakan ya shiga cikin fadinsa SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam: (Marowaci shi ne wanda aka ambata a kusa dashi amma ya kasa yi mini salati). Ahmad.

Share this:

Related Fatwas