Salatin Annabi (SallalLahu alaiHi w...

Egypt's Dar Al-Ifta

Salatin Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam)

Tambaya

Mene ne hukuncin yi wa Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) salati da sigar da ba ta a cikin Hadisai ba?

Amsa

Yi wa Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) salati da kowace irin siga abu ne da ya halatta, shin sigar ta zo a cikin Hadisai, ko ba ta zo ba, ko kuma tana cikin wadanda aka gwada aka ga amfaninsu, matukar dai ta dace da girma da darajarsa (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam).

Ba a la’akari da abin da wasu suke cewa na bidi’antar da wadannan sigogi; domin umurnin da Allah ya bayar na a yi masa salati a kuma roka masa aminci yana kunshe ne da bayyana girma da darajarsa, da girmama sha’aninsa, da daukaka mukami gami da matsayinsa; Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Saboda ku yi imani da Allah da manzonsa, ku kuma taimaka masa, ku kuma girmama shi) [al- Fathi: 9], haka ma Hadisai sun zo da umurnin kyautata yi wa Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) salati, Kaman inda ya ce: (Lallai ana bijiro mini da ku, a bayyana mini sunayenkun da sifofinku, saboda haka ku kyautata yi mini salati), sayyiduna Abdullahi Bn Mas’ud (Allah ya kara yarda da shi) ya ce: “Idan za ku yi wa Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) salati, to ku kyautata yi masa salati”. Allah Madaukakin Sarki shi ne masani.

Share this:

Related Fatwas