Tawassuli da Annabi (SallalLahu ala...

Egypt's Dar Al-Ifta

Tawassuli da Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam).

Tambaya

Mene ne hukuncin yin tawassuli da Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam)?

Amsa

Yin tawassuli da Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) abu ne da shari’a ta bayar da umurnin a yi, kuma al’ummar Musulmai na da da na yanzu suka yi aiki da wannan umurni, sai bai halatta a yi inkarin haka ba, akwai nassoshi masu yawa a cikin Alkur’ani da Hadisai da rubuce- rubucen malamai da suka tabbatar da haka.

A cikin nassoshin da suka zo akan haka akwai: Hadisin da Imam Nasa’i da Imam Tirmiziy da Imam Ibn Majah da wasu da dama suka kawo, cewa: wani mutum ya zo wurin Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) –wannan mutumin makaho ne- sai ya ce: ya Manzon Allah, Lallai Allah ya jarrabe ni da rashin ido, ka yi mini addu’a, sai Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce masa: (Ka yi alwalla, sannan ka yi sallah raka’a biyu, sannan ka ce: “Allahumma Inniy as’aluka, wa atawajjahu ilaika bi nabiyyika Muhammad, Ya Muhammad, inniy astashfa’u bika fi raddi basariy, Allahumma shaffi’in Nabiya fiyya) ya ce: (Idan ma kana da wata bukatar, ka yi irin haka), sai kuwa Allah Madaukakin Sarki ya dawo masa da idonsa.

Share this:

Related Fatwas