Sinadaren kara kyau, da kwalliya
Tambaya
Mene ne hukuncin yin aiki a kamfanonin da suke harhada sinadaren kara kyau da kwalliya?
Amsa
Asali a cikin komai shi ne halacci, in banda abin da nassin Alkur'ani ko Hadisi suka zo da bayyana haramcinsa, idan mace ta yi ado saboda mijinta, to wannan ado ne na halal wanda Allah Madaukakin Sarki ya halatta mata ta yi, shi kuma irin wannan adon a wasu lokuta tana bukatar ta yi amfani da wasu mayuka da kamfanonin da suke sana'anta sinadaren ado da kara kyau suke samarwa, a nan muna ganin babu laifi mutum ya yi aiki a wannan fagen, matukar dai aiki a wurin ba ya cutar da lafiyar dan Adam.