Hukuncin hikimar da take cewa: “Abi...

Egypt's Dar Al-Ifta

Hukuncin hikimar da take cewa: “Abin da gida yake bukata ya haramta ga Masallaci”

Tambaya

Mene ne Hukuncin hikimar da take cewa: “Abin da gida yake bukata ya haramta ga Masallaci”?

Amsa

Wannan hikimar da aka ambata, wadda ta yadu a tsakankanin Misrawa tana bayyana cigaban ilimi ne da yake kunshe da umurnin da shari’a ta wajabta wa kowani Musulmi jera bukatunsa daidai da muhimmancinsu, cikin azanci da hikima, a zahiri wannan hikima cewa take yi: babu batun yin sadaka sai idan mutum ya biya bukatun da suka wajaba akansa, ana kuma gabatar da gina mutum ne akan gina gini, kuma lallai an umurci mutum ne ya ciyar da dukiya a fagagen alhairi masu yawa, da suka hada da raya Masallaci, da taimakon talakawa da miskinai, da sauransu cikin hanyoyin alahairi, kowa ya yi daidai da yanayi da karfin da yake da shi, amma fa ya fara da bukatun kansa, sannan na wadanda alhakinsu ya rataya a wuyarsa, idan ya zama bayan ya yi haka akwai sauran dama, to zai iya fitar da shi zuwa ga wasu hanyoyin na alhairi cikin daidaito da wasadiyya.

Share this:

Related Fatwas