Yin addu’a lokacin saukar bala’i
Tambaya
Wacce karbabbiyar addu'a ake yi a yayin da wani bakin ciki ko bacin rai ya samu mutum?
Amsa
An so idan wani bakin ciki ko bacin rai ya samu mutum ya yi irin addu'ar da Annabi SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam yake yi a irin wannan yanayin, idan wani lamari na damuwa ya sameshi ya kasance yana cewa: "Ya Hayyu ya Kayyum, bi rahmatika Astaghith" Tirmizi, daga Anas Allah ya kara masa yarda.