Ta’addanci da tayar da fitina ta hanyar yaɗa ƙarya duka ayyuka ne na tashin hankali da lalata dukiyoyi da masu tsattsauran ra’ayi suke yi
Tambaya
Idan muna son mu yi wa ayyukan tashin hankali, da lalata dukiyoyi da masu tsattsauran ra’ayi suke yi suna, wane suna ya kamata mu ba su tsakanin “ta’addanci” da “yama- ɗiɗi”?
Amsa
Ta’addanci yana nufi tsoratarwa, kuma ya kasu gida biyu ne: Ta’addanci na tunani, wanda yake kasancewa ta hanyar kafirta Musulmi akan mas’alolin furu’a, ko a cikin mas’alolin da ya halatta a yi saɓanin fahimta game da su, sannan kuma akwai Ta’addanci na makami, wanda yake kasancewa ta hanyar tirsasa wa mutane bin ra’ayin masu tsattsauran ra’ayi ta hanyar aiki da ƙarfin makami. Shi ta’addancin tunani shi ne yake share wa ta’addancin makami fage. Shi kuwa yama- ɗiɗi, shi ma tsoratarwa ne, amma a mafi yawan lokuta yana nuni ne zuwa ga zaman ɗarɗar da damuwa da yake kasancewa bayan tsoro da razana, ba sharaɗi ne sai ya zama sakamako na tashin hankali da ayyukan ƙarfi kawai ba, hasali ma yana kasancewa ta hanyar yaɗa jita- jita da niyyar tunzura mutane, saboda haka kalmar yama- ɗiɗi ta fi zama daidai, kuma ta fi faɗi, kuma ba ta da wani sashe da za a iya sifanta shi da kyau, koda yaushe tana ɗauke ne da ma’ana mara kyau, saboda haka ne ma Allah Maɗaukakin Sarki ya ce: (Tabbas idan munafukai, da waɗanda zukatansu suke cike da cuta, da masu ‘yan yama- ɗiɗi masu yaɗa jita- jita a gari ba su daina ba, wallahi za mu ba ka umurnin ka bi ta kansu, sannan kuma ba za mu bari su cigaba da maƙwabtakar ba sai kaɗan. Tsinannu ne su, a duk inda aka same su a kama su, a yi masu mummunar kisa) [a- Ahzab: 60 -61], a nan Alƙur’ani ya kawo uƙuba ga wanda ya aikata haka.
Saboda haka, kalmar “Yama- ɗiɗi” ta fi dacewa a yi amfani da ita, amma duk da haka, mun aminta da kalmar “Ta’addanci”, muna kuma aiki da ita saboda ita ce ta fi yaɗuwa a cikin al’umma da ma wurin ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa a matsayin tarjamar kalmar “terrorism”.