Kafirta Hawarijawa

Egypt's Dar Al-Ifta

Kafirta Hawarijawa

Tambaya

Shin kafirta Hawarijawa muhimmin abu ne wajen yaƙarsu?

Amsa

Kafirta Hawarijawa ko rashin hakan bashi da tasiri wurin halaccin datse munanan ayyukansu da fuskantarsu da yaƙar ɓannarsu, domin kuwa an shar’anta yin jihadi ne a musulunci domin kare kai daga ta’addancin ɗan ta’adda kai tsaye, shin wannan ɗan ta’addan ya kasance musulmi ne ko ba musulmi ba, babu wani banbanci a Tsakani, daga cikin nassosin Al’ƙur’ani da suka fayyace wannan lamari akwai inda Allah maɗaukakin Sarki ke cewa: (Idan waɗansu ƙungiyoyi Biyu daga cikin muminai sun yayyaƙi junansu, to kuyi sulhu a tsakaninsu, idan kuma ɗayan cikinu ta zalunci ɗayan da yaƙi (wurin fara kai hari), to ku yaƙi wadda take neman a yi yaƙin don dawo da ita kan hanya har sai ta koma kan tafarkin Allah) [al-Hujurat: 9] Allah Maɗaukakin Sarki ya tabbatarwa da ƙungiyar da take zalunci siffar imani, duk da hakan amma ya bayar da umurnin a yaƙe ta, wannan ya zo ne sakamakon ta’addancinta da zaluncinta, don haka ne ma muke cewa : Lallai yaƙar Hawarijawa wajibi ne a shari’ance, domin kuwa akwai lada mai yawan gaske daga Allah Maɗaukakin Sarki, wannan halaccin kuwa ya zo ne sakamakon yanda suka rinƙa zubar da jinin mutanen da ba su ji ba kuma ba su gani ba, tare da yin ɓarna a doron ƙasa, haka nan sun ɓata sunan Addinin Musulunci wanda yake tsayayye, game da lamarin kafirci da Imani kuwa, lallai wannan –kamar yanda malaman Fiƙihu suka bayyana– yana da dangantaka da wasu abubuwa na addini da suka haɗa da: aure da saki, haka nan za a yi masa wankan gawa a kuma yi masa sutura, a yi masa sallah, sannan rufe shi a maƙabartun Musulmai,  za a kuma a raba gadonsa da dai sauran ire- irensu.

Share this:

Related Fatwas