Zahirin yi wa mata takwarkwasa

Egypt's Dar Al-Ifta

Zahirin yi wa mata takwarkwasa

Tambaya

Mene ne hukuncin yi wa mace takwarkwasa ko cutar da ita da lafazi ko da wani abu a jikinta?

Amsa

Ita dai mace rabin al’umma ce, ita ce warin namiji cikin mutumtaka, muhimmancinta a cikin al’umma bai gaza na da namiji ba, ita ce ma  rabin al’umma, kuma uwar raguwar al’umma, hakika Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) ya sanya alamar alherin maza ya ginu ne akan kyakkyawan mu’amalar da mace, sai ya ce: (Mafi cikan muminai wurin Imani shi ne masu kyawun hali a cikinsu, mafi alherin cikinsu kuma shi ne mafi alheri ga matayensu) Tirmizi ne ya ruwaito a “Al-Jame’I”.

To saboda haka ne ma Musulunci ya tsananta haramta yi wa mata takwarkwasa na batsa ko kokarin cin zarafinsu, an karbo daga Ma’akal bin Yasar – Allah ya kara masa yarda – ya ce:  Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) ya ce: (A soki kan dayan cikinku da allurar karfe shi ne mafi alheri gareshi da ya shafi mace da ba ta halasta gareshi ba) Dabarani.

Share this:

Related Fatwas