Hadisin “Al’umma ta zata karkasu”

Egypt's Dar Al-Ifta

Hadisin “Al’umma ta zata karkasu”

Tambaya

Shin Hadisin “Al’ummata zata kar kasu” yana nuni ne akan dukkan kashe kashe – wadanda ba za su tsira ba- wadanda aka siffantasu da cewa su ‘yan wuta ne, shin hakan yana nuni ne akan cewa su kafirai ne?

Amsa

Wannan Hadisin ya zo ta hanyoyi masu daman gaske da sashensu ke karfafa sashensu, don haka ne ma da yawan masana suka inganta wannan Hadisin, domin wasu malaman ma sun kai wannan Hadisin matsayin tawaturi a ma’anance.

Hakika wani sashe na masu karkata zuwa ga kafirta mutane sun dauki zahirin ma’anar wannan Hadisin ne ba ma’anarsa na ainihi ba, inda suka kafirta dukkan wanda ya sabawa wani sashe na lamuran akidu,  kai wasu daga cikinsu ma sun karkata akan haka da cewa lallai asalin wadannan kungiyoyin suna daga cikin al’ummar ijaba, don haka sabawar al’umma baya kai ta ga kafrici, kawai dai za ta fuskanci ukuba ne kamar sauran laifuffuka, kamar dai yanda aka sani, abin da ke nufi da (dukkansu suna wuta): ai za su shigeta ne kowa bisa gwargwadon halinsa da aikinsa saboda suna bijirar da kawunansu ne zuwa ga abin da yake shigar da mutum wuta, hakika wasu daga cikin malaman shari’a sun tabbatar da cewa Allah ba zai azabtar da kowa ba har abada.

Lafazin (Al’ummata zata karkasu zuwa gida saba’in da uku, dukkansu ‘yan wuta ne), akwai wani abun nuni da yake bayyana cewa su wadannan kashe kashen dukkansu ba su fita daga musulunci ba, domin Annabi SallaHu AlaiHi wa AliHi wa sallam ya sanya su daga cikin al’ummarsa, don haka a cikin tawilin wannan Hadisin ko da mutumin da yayi kuskure ne ko laifi baya fita daga musulunci, fadinsa (sai dai kashi daya kawai), abin nufi anan shi ne: su ne shiryayyu masu riko da sunnata da sunnar halifofi shiryayyu daga bayana, sune ma’abota ilimi na fiqihu, wadanda suke bin gurabun ayyukansa AlaiHis Salatu wassalam sau da kafa, ba su kirkiri wani abu na sauyi ko canji ba a addini, abin da ake nufi da karkasuwan al’umma shi ne karkasuwansu a usuli da akidu ba wai a rassa da ayyuka ba.  

Share this:

Related Fatwas