Matsayin magabata na ƙwarai game da...

Egypt's Dar Al-Ifta

Matsayin magabata na ƙwarai game da Hawarijawa

Tambaya

Mene ne matsayar magabata na ƙwarai game da Hawarijawa?

Amsa

Magabata na ƙwarai –fara daga Sahabban Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam)- sun yi mu’amala na ba- sani- ba- sabo ne da Hawarijawa, tun lokacin da suka bayyana a aikace a matsayin ƙungiya ta Musulunci a zamanin Imam Aliyu Bn Abuɗalib (Allah ya ƙara yarda da shi), a farko ya aika masu da Sayyiduna Abdullahi Bn Abbas, saboda ya bayyana masu ɓatar da suke ciki, ya kuma ba su amsa akan fahimtocin da suka shige masu duhu, waɗanda su ne suka yi sanadiyyar kaiwarsu inda suka kai, da yawa daga cikinsu sun tuba, sun yi watsi da tsauraran fahimtarsu, sauran kuma sun dage akan matsayarsu, da yin tawaye, sai Imam Aliyu ya ɗauki takobi ya yaƙe su, a matsaayinsa na halataccen shugaban Musulmai a wannan lokacin, saboda kuma ya zartar da wasiyyar Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) a inda ya ce: (.. su ne mafiya sharri a cikin mutane da dabbobi, madalla da duk wanda ya kashe, ko suka kashe shi, suna kira zuwa ga littafin Allah alhali ba su da wani matsayi a wurinsa, duk wanda ya yaƙe su ya fi su kusanci da shi..) [Abu Dawud].

Share this:

Related Fatwas