Rashin zurfin fahimta da bi sama- sama a ra’ayi dalilai ne da suke kai wa zuwa ga tsaurin ra’ayi da ta’addanci
Tambaya
Ta yaya ne rashin zurfin fahimta da bi sama- sama a ra’ayi suke kai wa zuwa ga tsaurin ra’ayi gami da ta’addanci?
Amsa
A cikin sifofin masu tsattsauran ra’ayi akwai rashin zurfin tunani da yin abu sama- sama, da yawa daga cikin Nassoshin Shari’a idan ka yi masu duba sama- sama za su kai ka ne zuwa ga saɓa wa abin da Allah da Manzonsa mai girma suke nufi, babban misali akan haka shi ne ma’anar bidi’a a wurin masu tsattsauran ra’ayi, inda suka ɗaura wa Hadisin Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) sama da abin da yake ɗauke da shi, a Hadisin: (Mafi sharrin abubuwa suke sababbinta, kuma dukan bidi’a ɓata ne) [Muslim], sun ɗauka cewa duk abin da Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) bai yi ba shi ne bidi’a kuma ɓata, sai suka ƙuntata wa kawunansu, suka kuma ƙuntata wa mutane, wannan kuma ba shi ne abin da Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yake nufi ba, sahabbansa ma bah aka suka fahimta daga gare shi ba, saboda dai bayan wafatinsa (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ne aka tattara Alƙur’ani a wuri ɗaya, sayyiduna Umar Bn al- Khaɗɗab (Allah ya ƙara yarda da shi) ya haɗa Musulmai su bi limami ɗaya a sallar Tarawihi, har ma ya ce: “Madalla da irin wannan bidi’ar”, Imam al- Shafi’iy wanda ɗaya ne daga cikin manyan jagororin magabata na ƙwarai ya bayyana cewa bidi’a ta kasu ne tsakanin Bidi’a mai kyau, da bidi’a abin zargi, kawai dai ta’assubanci da makauniyar biyayya ce ta hana masu tsattsauran ra’ayi bin gaskiya, ta kuma toshe masu hanyarta.