Tsofaffin fahimta da aka gada da ta...

Egypt's Dar Al-Ifta

Tsofaffin fahimta da aka gada da tasirinsu wajen yaɗuwar ta’addanci

Tambaya

Shin jawo tsofaffin fahimta na da da aka gada sun yi daidai da yanayin da ake ciki? Mene ne tasirin yin haka wajen yaɗuwar ta’addanci?

Amsa

Yanayin da ake ciki yana da matuƙar tasiri wajen samar da fahimta ta Fiƙihu da ma fitar da fatawa a Shari’ar Musulunci, wannan yana ɗaya daga cikin dalilan samun mataki – mataki a cikin hukunce- hukuncen Shari’a, alal misali, yanda sallah take a farkon lokacin da aka shar’anta ta bah aka take a ƙarshen lokacin da aka aiko Annabi ba, an ruwaito Hadisi daga Abdullahi Bn Mas’ud (Allah ya ƙara yarda da shi) ya ce:  A da mukan yi wa Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) sallama yana sallah, ya kuma amsa mana, lokacin da muka dawo daga wurin An- Najjashi, mun yi masa sallam, amma bai amsa man aba, sai ya ce: (Lallai aikin mai sallah shi ne ya shagalta da sallarsa) [al- Bukhari da Muslim], a cikin bala’o’in da ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi suke kawowa akwai kasancewars ba sa la’akari da yanayin da ake ciki, sun ɗauka cewa duk wani yanayi da ya saɓa da yanayin da Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya rayu a cikinsa, to yanayi ne abin zargi, suna kuma yin duk abin da za su iya wajen sauya shi, su kuwa manyan malamai magabata ba su aikata haka ba, hasali ma sun saɓa wa magabantansu a mas’aloli masu yawa suna la’akari da yanayin da suka tsinci kawunansu a ciki, litattafansu cike suke da haka, abin ya zama wajibi akanmu shi ne mu yi koyi da su, mu kula da yanayin da muke ciki, kada mu jajibo ijtihadinsu mu yafa wa yanayin da muke ciki ba tare da lura da abin da ya bambanta su ba, wannan kuma shi gudummuwar da malamai masana za su bayar.

Share this:

Related Fatwas