Mu’amala da litattafan Fiƙihu da aka gada a matsayin cewa gaba ɗayansa ya tabbata shi ne ɗaya daga cikin dalilan aukawa cikin fahimtar Hawarijawa
Tambaya
Mene ne ya sanya yin mu’amala da litattafan Fiƙihu da aka gada a matsayin cewa gaba ɗayansa ya tabbata ya zama ɗaya daga cikin dalilan aukawa cikin fahimtar Hawarijawa?
Amsa
Mu’amala da litattafan Fiƙihu da aka gada a matsayin cewa gaba ɗayansa ya tabbata kuskure na babba, saboda da yawa daga cikin hukunce- hukuncen Shari’a suna matuƙar tasirantuwa da zamani da wuri, wannan Magana ce da ɗaukacin malamai suka haɗu akanta, idan sauyi ko saɓanin zamani da na wurin ba mai yaw aba ne, ta yiwu fatawa ko hukuncin Shari’a su zama ba su tasirantu da wannan sauyi ko saɓani ba, za mu iya ganin wannan a shekaru dubu ɗaya da ɗari biyun farko na Musulunci, idan muka gwada babban sauyi da saɓanin da ya samu bayan juyin juya halin sadarwa da zirga- zirga da suka faru a ƙarnoni biyun ƙarshen nan. Wannan sauyin ba wai kawai sauya duniya ya yi kawai ba, hasali ma sai da ya sanya saurin na wuce hankali a cikin wannan sauyi; abin da zai sanya dole malaman kowane zamani su zama su ma suna bibiyan wannan sauyi da sauri, wajen sanya hukunce- hukuncen Fiƙihu da za su yi daidai da yanayin da ake ciki na wannan sauyi da yake faruwa cikin gaggawa, wannan ne kuma abin da masu tsattsauran ra’ayi ba su ma san shi ba, su a wurinsu wannan sabon duban fita daga mazhabar magabata ne, kai ma alal haƙiƙa wannan shi ne ainihin mazhabarsu, dalili akan haka shi ne sun saɓa wa magabatansu saboda faruwar sauyi a cikin yanayin da suke ciki.