Gudummawar hankali wajen fahimtar A...

Egypt's Dar Al-Ifta

Gudummawar hankali wajen fahimtar Alƙur’ani da Hadisai da samar da ingantaccen manhaji

Tambaya

Mene ne gudummawar hankali wajen fahimtar Alƙur’ani da Hadisai da samar da ingantaccen manhaji?

Amsa

Hankali shi ne abin da ake iya riskar abubuwa da shi, a kuma yi zaɓi, kishiya ne na gariza, da kuma shi ne ɗan Adam ya bambanta da sauran halittu masu rai, ba shi ne ƙwaƙwalwar da take a kai ba, duk kuwa da cewa suna da dangantaka, Allah Maɗaukakin Sarki ya ce: (Shin mene zai hana su yi tafiya a bayan ƙasa, ta yanda za su zama suna da zukatan da za su rinƙa hankaltuwa da su..) [al- Hajji: 46]. Da hankali ne manyan malaman Musulunci suka tabbatar da wasu manyan abubuwa da addini ya ginu akansu, kaman wajibci samuwar mahalicci ga waɗannan halittun, da kuma wajibcin tsarkakarsa ga barin abokin tarayya, da wajibcin sifantuwarsa da dukan kamalar da ta dace da shi mai girma da ɗaukaka, da kuma rashin sifantuwarsa da duk wani abu da yake da naƙasa da aibi, da wajibcin sifantuwar Manzanninsa masu girma da sifofin gaskiya da amana da kaifin hankali. Lallai hankali yana da babbar rawar da yake takawa wajen fahimtar daidai da abu mai muni, hankali ne yake riskar kyawon gaskiya da karamci, da kuma munin ƙarya da rowa, saboda haka ne masu hankali a dukan zamunna da wurare suke yabon gaskiya, suke kuma aibata ƙarya. Game da hukunce – hukuncen Fiƙihu ba hankali ne ya samar da su ba, amma dai shi ne yake istinbaɗinsu ya kuma fahimce su daga nassoshin Shari’ar Musulunci, a ƙarƙashin wasu ƙa’idoji na harshe da na Usulu da ƙa’idojin istinbaɗi da malamai suka bayyana..

Share this:

Related Fatwas