Shari’ar Musulunci ilimi ne da yake...

Egypt's Dar Al-Ifta

Shari’ar Musulunci ilimi ne da yake da asali

Tambaya

Shin Shari’ar Musulunci ilimi ne da yake da asali, ko kuma kawai wani tunani ne da ya halasta ga kowa da kowa ya kutsa cikinsa da komarsa?

Amsa

Babu wata dama a shai’ar Musulunci da ta bai wa wani mutum ikon kutsawa cikin hukunce hukuncen shari’ar Musulunci matukar ba yana daga cikin masana shari’ar ba ne, domin dai shari’ar Musulunci na da tsari da ilimi mai asali da ka’idoji da aka fitar daga nassoshin Al’kur’ani Mai girma da Tsarkakakkiyar sunnar Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) tare da hukunce hukuncen da Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya yanke, haka nan fahimtar sahabbai (Allah ya kara yarda da su); domin hakan wani asali ne da shugabanni da malamai suka fitar suka rubuta wannan ilimi a cikin littafansu, haka nan malaman fikihu sun iyakance manhajin da mutum zai iya koyon ilimin shari’a da usulun shari’ar ga wanda yake so, duk wanda ya shagaltu da wani abu sabanin haka, ko ya gaza koyon ilimin, to ya yi aiki da fadin Allah Madaukakin Sarki: (Ku tambayi ma’abota sani idan kun kasance ba ku sani ba) [An’nahli: 43], saboda haka daga cikin matsalolin masu tsattsauran ra’ayi shi ne kutsawa cikin abin da ba su sani ba, sannan ba iya haka lamarinsu yake tsayawa ba, ai har farlanta ra’ayinsu na kuskure suke yi ga wadanda suke kusa da su, ba iya haka suke tsayawa ba, ai suna ma sabawa gami da sukar malaman gaskiya tare da ikirarin cewa sun sayar da addininsu da duniyarsu, da a ce sun karanci shari’a da usulunta bisa manhajinta da ake bi tun daga lokacin magabata zuwa wannan lokaci, to da ba su sabawa malaman shiriya ba, da kuma sun san girmansu da darajarsu.

Share this:

Related Fatwas